Wasu mazauna garin Gaidam sun ce harin na jiya shine na cikon takwas a cikin watanni 13 da maharan ke kai wa garin, amma duk harin nasu basu ci nasara ba.
Tun da mislain karfe biyar na yammacin jiya ne suka fara jin harbe harben bindiga, lamarin da ya takaita harkokin jama’a kowa ya shige gida, amma har kusan goma sha biyu na dare ana jin karar harbe harbe.
Bayanai daga garin Gaidam na nuni da cewa mayakan sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan kwastam guda uku, amma babu wani karin haske daga bangaren hukumomin kwastam din.
Mai magana da yawun jami’an ‘yan sandan jihar Yobe Abdulkarim Dungus ya tabbatarwa Muryar Amurka da aukuwar wannan lamari duk da cewa ya ce bai ji daga bangaren kwastam ba, amma rahotanni da suke samu daga wurin jami’an su sun shaida musu hakan.
Dungus ya ce “wannan wani harin ba-zata ne suka kai ba kamar yanda aka saba gani, sun shigo ne farab daya suka fara bude wuta, inda sojoji suka fito suka yi artabu da su, har ma jirgin yakin sojoji ya kawo dauki domin fatattakar maharan.”
Ya ce duk da haka maharan sun yi nasarar fasa shaguna daya zuwa biyu wanda har yanzu ba a iya tantance adadin shagunan da aka fasa ba, sai kuma batun awaon gaba da ma’aikatan kwastam guda uku kana babu wani rahoto a kan ko wani ya mutu ko kuma wani ya samu rauni, kana ba a yi kone kone kamar yanda suka saba ba.
Wasu mazauna garin na Gaidam sun fadawa wakilin Sashen Hausa yanda al’amarin ya faru. Sun tabbatar da babu wanda aka jiwa ciwo haka zalika babu wasu kone kone da ‘yan ta’addan suka yi. Sai dai wasu ‘yan ta’addan sun samu munanan raunuka daga fatattakar da sojoji suka musu.
Ga dai Rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Boko Haram, jihar Yobe, Nigeria, da Najeriya.