Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Kwamandan Sojan Najeriya da 'Yan Boko Haram Suka Kashe


A cikin wani hali na juyayi da alhini, an yi jana'izar marigayi Kanar Dahiru Ciroma da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne su ka kashe shi yayin da ya ke wani sintirin tabbatar da tsaro a Danboa, jahar Borno.

Anyi Jana’izar Kanar Dahiru Ciroma Bako, kwamandan sojan Najeriya da 'yan Boko Haram suka kashe a garin Damboa dake jihar Borno a shiyyar arewa masu gabashin Najeriya.

Marigayi Kanar Bako ya mutu ne bayan kwantan-baunar da mayakan Boko Haram suka yi wa tagawarsa a yankin Sabon Gari-Wajiroko, kusa da Damboa, jihar Borno jiya.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana Kanar Bako a matsayin jarumi, jajirtacce a wurin aikinsa na Soja, kuma wanda bashi da tsoro. Ya kara da cewa, marigayi kanar Bako mutum ne da ya san ya kamata, kuma yana daya daga cikin wadanda suka karya lagon 'yan kungiyar Boko Haram a jihohin Borno da Yobe.

Gwamnan na jihar Borno ya ce, gwamnati zata yi iya kokarinta wajen ganin ta tallafawa iyalan marigayin.

Mazauna garin Damboa na ta nuna alhinin kan rashin marigayi kanar Bako.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG