Cikin manyan mutanen da su ka halarci wannan hidima ta gwamnan na jihar Borno, har da Mai Kanuribe na Lagos, Alhaji Mustapha Muhammad. Tawagar Mai Kanuribe din riga tawagar gwamna tashi daga wurin hidimar. A kan hanya ta yi hatsari har shi Mai da wasu mutane uku cikin tawarsa su ka rasu.
Tawagar Gwamnan ta zo ne ta tarar da hatsarin ya auku kuma ta kai dauki.
Gwamnan tare da Sanata Kashim Shettima da wasu shugabanni, sun gamu da hatsarin a kan hanyarsu ta dawowa daga Mafa kuma kamar yadda aka zata, gwamnan da wadanda ke tare da shi, sun bi gawarwakin Mai, da sauransu, zuwa ga danginsu a Maiduguri, su na masu tausaya wa dangin wadanda suka rasa rayukansu. Kuma ya halarci jana'izar.
Gwamna Zulum yana mai cewa marigayi Mai Kanuribe, shugaba ne mai son ci gaban Borno da jama'arta, ya yi tafiyarsa ta ƙarshe zuwa Mafa, don girmama gwamnatin Zulum da APC.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta kurakuran Mai, da wadanda suka mutu tare da shi, ya kuma shigar da su duka a Aljanna Firdausi.
Ga karin bayani daga Haruna Dauda cikin sauti: