SKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka fatattaki ‘yan bindiga tare da ceto mutanen da suke garkuwa da su fiye da 30 a jihar kebbi.
Yankin kudancin jihar Kebbi na daga cikin yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya da jama'a suke fuskantar cin zarafi daga ‘yan bindiga, kamar yankunan Bena, Wasagu, Fakai, Mahuta da dai sauransu.
To sai dai a karshen makon da ya gabata rahotanni sun nuna cewa dakarun Sojin Najeriya sun kai farmaki a sansanonin ‘yan bindiga dake yankunan kuma sun samu galaba a kan barayin.
Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Hussaini Aliyu Bena wanda a farko ya sanar da cewa an ceto mutane 30 da aka yi garkuwa dasu, ya ce bayanan baya-bayan nan sun nuna adadin mutanen da dakarun suka ceto ya haura 30 abinda ya ta'allaka ga kwarin guiwa da gwamnati mai ci yanzu a jihar ke baiwa jami'an tsaro.
A dayan bangare kuwa a jihar Sakkwato dake makwabtaka da jihar Kebbin wasu jama'a ne ke nuna fargaba a kan wani samame da suka ga jami'an tsaro sun kai a wani wuri kuma suka kama mutanen da suke tuhumar munanan ‘yan ta'adda ne, inda muka samu zantawa da daya daga cikin masu fargabar.
Sai dai kakakin Rundunar 'yan sanda a jihar Sakkwato ASP Ahmad Rufa'I ya ce basu kai ga samun labarin ba.
Yankuna da dama ne a Najeriya ke fama da matsalolin rashin tsaro, inda mutane ke cike da bukatar samun magance matsalolin domin samun ci gaba.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5