WASHINGTPN, D. C. - An tabbatar da mutuwar Huzeifa a ranar Lahadin da ta gabata bayan wani samame da aka kai a yankin Indelimane, in ji su, amma ba su yi karin bayani a kai ba.
Shirin bayar da tukwici don tabbatar da adalci na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na tayin tukwicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Huzeifa, saboda zarginsa da aka da taka rawa a harin da aka kai a makwabciyarta Nijar a shekarar 2017, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da IS sun yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasashen Mali da Nijar, da kuma makwabciyarta Burkina Faso, lamarin da ya janyo rashin zaman lafiya a yankin Sahel na yammacin Afirka.
Ya zuwa watan Maris, matsalolin tsaro da na jinkai da aka dade ana fama da su ya raba sama da mutane miliyan uku da muhallansu a yankin, a cewar Kungiyar Kula da Hijira ta Duniya.
-Reuters