Sojojin Kamaru Sun Mikawa Sojojin Najeriya Wasu Yan Boko Haram

Daraktan wasa labarai na rundunar sojan Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, yace dakarun Kamaru sun ziyarci takwarorinsu na Najeriya, a ci gaba da kawancen aiki tare inda har suka kamo yan Boko Haram suka kuma mikawa dakarun Najeriya.

Akwai hadin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da makwabtansu a karkashin hukumar tafkin Chadi, Sojan Najeriya da na Kamaru suna hadaka domin yaki da yan Boko Haram.

Kanal Kuka Sheka, yace rundunar sojan Najeriya na takaicin hadarin da dakarun Kamarun suka fuskanta yayin da suke komawa gida, inda suka taka wani bom da aka binne akan hanyar dake tsakanin Pulka zuwa Ngoshe, har wani hafsan sojon Kamaru yaji ciwo hade da wasu sojoji takwas.

Haka kuma Sojojin Kamarun sun ceto wasu mata da kananan yara akan hanyar su ta komawa gida.

Sai dai shi wannan hafsa da yaji ciwo ya rasu yayin da ake kokarin daukar sa a jirgi zuwa Duwala na kasar Kamaru.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Kamaru Sun Mikawa Sojojin Najeriya Wasu Yan Boko Haram - 1'55"