Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Boko Haram Sun Kai Hari Wasu Kauyuka Dake Kan Iyar Najeriya Da Kamaru


US Soldiers in Cameroon - Boko Haram
US Soldiers in Cameroon - Boko Haram

Rahoanni daga jihar Adamawa Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa wasu yan bindiga da ake kyautata zaton cewa yan Boko Haram ne sun sake kai wani hari akan wasu kauyuka dake kan iyakar Najeriya da Kamaru, ta yankin Madagali.

Dakarun kasar kamaru nema suka sami nasarar tarwatsa yan bindigan, koda yake an samu asarar rayuka. Yanzu haka dai ‘yan bindigar sun sauya salo na shiga lunguna lungunan da babu sojoji, kuma su kan ci karensu ne babu babbaka, kamar wannan hari da suka kai wanda har yanzu ba a tantance rayukan da suka kashe ba.

Wani mazaunin wannan yanki ne ya tabbatar wa da wakilin Muryar Amuraka Ibrahim Abdul’aziz, faruwar wannan lamari har ma ya kara da cewa wasu mazauna yankin na barin garin a halin yanzu, ya kuma ce dakarun Kamaru ne kadai ke taimaka musu kasancewar suna kwana akan Duwatsu dake yankin.

Shima ‘Dan Majalisar Wakilai dake wakiltar mazabar Michica da Madagali, Hon. Adamu Kamale, ya tabbatar da faruwar wannan sabon harin da aka kai, ya kuma ce yanzu haka akwai sauran wasu kauyukan da yan Boko Haram kanyi shawagi kasancewar babu sojoji.

Yanzu haka dai yan sa kai na Maharba da kuma yan Banga ne ke tallafawa sojoji a wadannan yankuna, daya daga cikin kwamandan yan sa kan ya fadawa Wakilin mu cewa har yanzu suna samun ‘yan bindigar na shigo ta wasu hanyoyi akai akai.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG