Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musayar Kalamai Game Da Ci Gaban Shugabancin Bukola Saraki


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Sarki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Sarki

Kiran da wasu yan Majalisar Dattawa sukayi ga shugaban Majalisar Bukola Saraki, domin ya sauka bayan fuskantar zargin rashin bayyana kaddarorinsa ga kotun da’ar ma’aikata, ya sanya dan majalisa dake matukar mara masa baya maida martani.

Tuni ma dai shugaban kwamitin labarun majalisar Sanata Aliyu Sabi, yace ba ayi kiran bisa manufa mai kyau ba ne, in za a tuna kotun koli ta ‘ki amincewa da bukatar Sanata Bukola kan hana kotun da’ar ma’aikata ci gaba da yi masa bincike kan mulkin sa tun yana gwamnan jihar Kwara.

Masu tunanin ko Saraki na dagewa kan zama a kujerar shugaban Dattawa ne don ya kara karfi don ya nemi shugabancin Najeriya a shekara ta 2019, wannan batu ba gaskiya bane, inji mukarrabin Sarakin Sanata Isa Hamma Misau, har ma yace su shugaba Buhari suke marawa baya.

Mukaddashin shugaban kwamitin amintattun PDP Sanata Wali Jibrin, yace zasu tsayar da dan takarar su daga Arewa a shekara ta 2019, don fuskantar APC. Yana mai nuna farin jinin PDP ma ya fara dawowa.

Duk da dai riga mallam masallaci ne batun zaben 2019, ga masu niyyar takara ko marawa wani baya amma tuni siyasar Najeriya ta fara tafiya da batun wannan zaben. Zuwa yanzu dai shugaba Buhari na dagewa ne kan yaki da wadanda ake zargi sun karkatar da kudin sayen makamai fiye da dala miliyan dubu biyu, kuma babu alamun yana nuna alamar neman zarcewa.

Don karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG