Sanarwar da Mr. B. D. Lawal ya sawa hannu tace wadanda shugaba Buhari ya amince da saukesu sun hada da shugaban telibijan na kasa wato NTA
Sauran su ne shugaban Radiyon Najeriya da aka sani da suna FRCN da shugaban Radiyon Muryar Najeriya ko VON.
Shugaban dillancin labarai ko NAN shi ma ya tafi haka ma takwaransa na hukumar dake kula da kafofin yada labarai wato NBC.
Shi ma na hukumar wayar da kawunan 'yan kasa ko NOA bai tsira ba. Dukansu suna karkashin ma'aikatar yada labarai ne.
Bayan wadannnan snarwar ta gwamnati ta sanarda sallamar karin wasu shugabannin hukumomin gwamnati guda ishirin. Shugabannin da aka sallama an gargadesu su mika ragamar ikon inda suke ga masu mukami mafi girma dake biye dasu kafin a nada sabbin shugabannin.
Malam Garba Shehu na fadar shugaban kasa ya bayyana dalilin sallamar mutanen a wannan lokacin. Yace akwai shugabannin fiye da dari na hukumomin gwamnati Duk sai da aka gwadasu a ga ko zasu iya aiki da wannan sabuwar gwamnatin. Cikinsu ne aka sauke su 26.
Mr. Mike Omeri na hukumar wayar da kawunan jama'a ko NOA da aka saukeshi yace sun gode da zarafin da suka samu na yin aiki. Yace mutum bai cika goma. Yace akwai wasu abubuwa da basu yi daidai ba da fatan wadanda zasu zo daga baya zasu yi da kyau.
Ga karin bayani.