Rundunar sojan Iraqi ta fada yau Laraba cewa dakarunta sun sake kwato karin wurare daga hannun mayakan kurdawa, ciki harda madatsar ruwan birnin Mosul, bayan wani farmaki da suka kai wurin don kwato birnin Kirkuk da wasu filayen hakar mai a arewacin kasar.
Kurdawa sun kwace ikon birnin a shekarar 2014 a lokacin da mayakan ISIS suka kai wasu hare-haren mamaya ta arewaci da yammacin kasar. Gwamnatin kasar ta bukaci kurdawan su saki ikon wuraren, daga nan ta dauki mataki bayan da hukumomin kurdawan suka yi watsi da zancen, sai ma suka ma jefa kuri’ar raba gardama akan neman ‘yancin gashin kai a watan da ya gabata.
Dakarun Iraqi basu fuskanci wata tirjiya ba sosai, saboda mayakan kurdawan sun ja da baya ba tare da maida murtani ba a yawancin wuraren da dakarun suka sake kwatowa cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Sassan biyu sun yi aiki tare a fagen daga, a gwabzawar da aka yi don kawarda ISIS a Iraqi, kuma kowanne bangare ya sami goyon bayan soji daga Amurka.