Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Bangladesh Sun Fara Tantance 'Yan Jinsin Rohingya dake Isa Kasar


'Yan Rohingya da suke arcewa daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh
'Yan Rohingya da suke arcewa daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh

Tantance 'yan gudun hijiran Rohingya da Bangladesh ta fara yi ya rage kwarararsu daga Myanmar amma ya bar wasu kimanin dubu 15 cikin kududdufi ba tare da ababen rayuwa ba

Kwararar da ‘yan gudun hijirar Myanmar ke yi ya ragu a jiya Talata yayin da hukumomin kasar Bangladesh suka fara tantance sabbin ‘yan jinsin Rohingya da ke isa kasar, lamarin da ya haifar da tsaiko, ya kuma bar mutanen da aka yi kiyasin sun kai dubu 15 a wani yanki mai kududdufi ba tare da ababan bukatar rayuwa ba, in ji wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.

Hare-hare akan ‘yan kabilar Rohingya a arewacin jihar Rakhine ya samo asali ne bayan abkawa wasu ofisoshin ‘yan sanda 30 da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Arakan Rohingya suka yi a ranar 25 ga watan Agusta

‘Yan gudun hijirar da aka kiyasin sun kai dubu 582, wadanda kashi 60 yara ne, suka isa Bangladesh, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa an samu sabbin masu kwarara zuwa kasar a daren Lahadin da ta gabata.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce wasu sabbin hotunan tauraron dan adam da aka fitar, sun nuna an kona baki daya ko kuma rabin kauyuka 288 a jihar Rakhine.

An kuma zargi dakarun Myanmar da aikata kisan kare dangi da fyade da kwashe kayayyakin jama’a da dasa nakiyoyi a hanya domin hana mutane komawa gidajensu.

Wani hoto da jirgi mara matuki na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya dauka, ya nuna dubban ‘yan kabilar Rohingya sun yi layi na tsawon kilomitoci a wani yanki da ke zagaye da kududdufai a kudancin Bangladesh.

Hukumar ta bayyana damuwa kan halin da wadanda lamarin ya rutsa da su ke ciki, wadanda ba su da abinci ba da ruwan sha, ba su kuma da mafaka yayin da mafi aksarinsu suke cikin gajiya bayan kwashe mako guda da suka yi suna tafiya a kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG