Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Kai Hari Kan Cibiyar Horas Da Yan Sanda A Afghanistan


Afghanistan
Afghanistan

An kai hare hare masu kama da juna a kan jami'an Yan sandan Afghanistan.

Kimanin mutane 52 ne suka mutu wasu 200 suka jikkata sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai kan cibiyar horas da yan sanda a gabashin Afghanistan a yau Talata.

Jami’ai suka ce an fara kai harin ne lokacin da d'an kunar bakin wake ya tada nakiyoyi da aka makarawa wata mota a kusa da cibiyar hosarwar a Gardez, babban birnin lardin Paktia. Bayan tashin bam din gungun yan ta’addan suka kutsa cikin cibiyar inda sukayi musayar harbe harbe da yansanda.

Daraktan harkokin lafiyar jama’a na birnin, Hedayatullah Hamedi, ya fadawa manema labarai cewa al’amarin ya shafi fararen hula da kuma Yan sanda.

Wata majiya daga gwamnatin yankin na Paktia yace shugaban rundunar Yansandan yankin, Toralia Abydani na daga cikin wadanda aka kashe a harin.

Tuni Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

An dai kai wani makamancin irin wannan harin a yau Talatar a barikin Yansanda a Kudancin Yankin Ghazni. Kafar dillancin labarai ta Associated Press tace a kalla yan sanda Bakwai aka kashe a harin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG