Sojojin Amirka zasu janye daga Iraq karshen 2011

Shugaba Barack Obama na Amirka

Shugaba Obama yace za' janye sojojin Amirka daga Iraq a karshen wannan shekara.

Shugaban Amirka Barack Obama ya bada sanarwar cewa za’a janye dukkan sojojin Amirka daga Iraq a karshen wannan shekara.

A yau juma’a shugaban ya bada wannan sanarwa bayan ganawar da yayi ta hoton vidiyo da Prime Ministan Iraq Nouri Al Maliki

A furucin da yayi a fadar shugaba ta White House, shugaba Obama yace ko tantanma sojojin Amirka zasu yi bikin kirisimeti a gida. Yace shi da Prime Ministan Iraq sun yarda da haka.

Mr Obama yace dangantakar Amirka da Iraq zata shiga wani sabon babi bisa mutunta juna da kuma bukatu daya. Yace Amirka da Iraq zasu aiki tare domin tabbatar da matakan tsaron yankin, ya kuma kara da cewa Amirka tana sa ran sauran kasashe zasu mutunta diyaucin Iraq.

A shekara ta dubu biyu da uku aka fara yaki a Iraq, a zaman daya daga cikin yakin da Amirka ta fi dadewa tana yi a tarihinta. Foye da sojojin Amirka dubu hudu da dari hudu ne suka mutu a wannan rikici.