Yariman Saudiyya mai jiran gado Sultan Bin Abdul-Aziz ya rasu da wata cutar da ba a bayyana ba. Ya rasu ya na da shekaru tamanin da ‘yan kai.
Kafofin yada labaran kasar Saudiyya ne su ka bada sanarwar, su ka ce ya rasu ranar asabar a wata kasar waje bayan ya yi fama da rashin lafiya. Amma kafofin yada labaran kasashen Turai sun ce ya rasu ne a birnin New York inda ya ke jiyya.
Marigayi Yarima Sultan mai jiran gado na daga cikin manyan jami’ai mafiya tasiri a Masarautar ta Saudiyya. Uban su daya da sarki Abdullah.
A karshen shekarar 2010 ya yi mulkin Saudiyya lokacin da Sarki Abdullah ya yi zaman jiyya a birnin New York bayan an yi mi shi wani aikin fida. A ‘yan shekarun nan sarkin da yariman dukan su biyu sun yi fama da matsalolin rashin lafiya.
A shekarar dubu biyu da 9, marigayi yarima Sultan ya zo nan Amurka ya yi jiyyar wata cutar da ba a bayyana ba. Amma kafin zuwan na shi nan Amurka likitoci sun ce ya kamu da cutar sankara.
Bayan rasuwar yariman, sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce an yi rashin babban shugaba kuma dadadden babban abokin Amurka. Daga Tajikistan ta yi wannan furuci a yau asabar, inda ta yada zango a rangadin da take yi a kasashen tsakiyar nahiyar Asiya.
Marigayi Sultan bin Abdul-Aziz shi ne ministan tsaro da na ma’aikatar jiragen saman kasar Saudiyya tun a shekarar 1963. Ofishin jakadancin Saudiyya a nan Washington DC,ya ce shi ne jigon zamanantar da rundunonin mayakan masarautar Saudiyya.
A wani lokaci can baya ya rike mukamin ministan sufuri kuma ya yi gwamnan Riyadh.
Kafofin yada labaran Saudiyya sun ce ranar talata za a yi jana’izar yarima Sultan a Riyadh.
Jami’an gwmanatin kasar Saudiyya ba su yi sanarwar cewa ga magajin yariman marigayi ba. Amma ga dukan halamu wanda zai maye gurbin na shi shi ne Yarima Nayef ministan cikin gida. A shekarar dubu biyu da 9 aka nada shi mataimakin frayim minista na biyu, ga al’adar masarautar wannan mukami ne da ake baiwa masu jiran gado.