Sojoji Sun Kama Wani Da Ake Zargin Dan Ta'addar Boko Haram Ne A Taraba

Sojojin Najeriya yayin wani atisaye da suka yi (Twitter/@HQNigerianArmy)

Bincike ya bayyana cewa Yakubu wanda ke sana'ar sayar da abinci, yana baiwa 'yan ta'addar Boko Haram din da aka tura jihar Taraba mafaka domin aikata ta'addanci.

Dakarun burged ta 6, na rundunar sojin Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya mai taken "Operation Whirl Stroke" a shiya ta 3, sun kama wani da ake zargin dan ta'addar Boko Haram ne a kauyen Garba Chede na karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

An kama wanda ake zargin da aka bayyana da Nura Yakubu ta hanyar amfani da sahihan bayanan sirri.

Bincike ya bayyana cewa Yakubu wanda ke sana'ar sayar da abinci, yana baiwa 'yan ta'addar Boko Haram din da aka tura jihar Taraba mafaka domin aikata ta'addanci.

Sanarwar manema labaran da Kyaftin Olubodunde Oni wanda ya kasance mataimakin daraktan hulda da jama'a na burged ta 6 yace karin bayanan da aka samu sun alakantashi da kungiyarsa da laifin yin garkuwa da wani dan kasuwa, Arinze, da kuma dan Alhaji Ibrahim wani lokaci a baya a kauyen Garbatau dake karamar hukumar ta Bali.