Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Sokoto: Shelkwatar Tsaron Najeriya Ta Zargi Wata Fashewa Ta Daban Da Kisan Kimanin Mutane 10


 Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba
Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

Manjo Janar Edward Buba, yace wata fashewa ce ta daban ta haddasa mace-macen da jikkatar amma ba dalilin hare-haren kai tsaye ba.

Shelkwatar tsaron Najeriya ta zargi abin da ta bayyana da "wata fashewa ta daban" da kisan kimanin mutane 10" sakamakon hare-haren Sokoto.

A 'yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin Sokoto tace hare-haren soji sun hallaka kimanin mutanen kauye 10 tare da jikkata wasu a karamar hukumar Silame ta jihar.

Sai dai daraktan yada labaran shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, yace wata fashewa ce ta daban ta haddasa mace-macen da jikkatar amma ba dalilin hare-haren kai tsaye ba.

"Yanzu, ina batun wata fashewa ta daban. Saboda daya daga cikin wuraren da aka hara ma'ajiyar makaman 'yan ta'adda ce dake kauyen. Idan ina maganar ma'ajiya, ina nufin tarin makamai da turakun da aka ajiye a wurin," kamar yadda ya bayyana a jawabinsa yayin ganawa da manema labarai a shelkwatar tsaron dake Abuja a yau Juma'a.

"Don haka, a ka'ida duk inda harsashi ya afka kan makami za a samu fashewa ta 2 wacce za ta sabbaba farfashewa tare da watsuwar abubuwa a iska wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 10 da aka ba da rahoto. Ba hare-hare ta sama ne suka hallaka mutanen kai tsaye ba.

"Mutanen da harin ya samu kai tsaye sune 'yan ta'addar Lakurawa, kuma gawarwakinsu sun babbake har ba a iya ganesu."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG