Sojoji da Jiragen Saman Yakin Najeriya Sun Kai Hari Kan ‘Yan Boko Haram Cikin Wani Daji

Rundunar ta ce ta kashe ‘yan bindiga 56 a farmaki kan wasu sansanoni a dajin Alafiya, kimanin kilomita 21 daga garin Bama a Jihar Borno
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kasha abinda ta kira “’yan ta’adda” su fiye da 56 a cikin wani daji mai suna Alafiya, inda aka yi imanin ‘yan Boko Haramn sun kafa sansanoni.

Wata sanarwar da hedkwatar ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayar ta ce jiragen saman yaki da kuma sojojin kasa, sun kaddamar da farmaki kan sassa dabam-dabam cikin wannan daji dake da tazarar kilomita 21 daga garin Bama, inda ta kasha ‘yan ta’addar.

Sojoji biyu sun samu raunuka, amma ba a bayyana tsananin irin raunin da suka samu ba.

Rundunar sojojin ta ce ta kai wadannan hae-haren ne domin wargaza kokarin da ‘yan Boko Haram suke yin a kafa sabon sansani a wannan wurin.

Har yanzu ana ci gaba da luguden wuta a kan wuraren da aka ga alamun ‘yan bindigar na Boko Haram cikin wannan daji.

Haka kuma, sojojin dake cikin rundunar hadin guiwa ta kasa da kasa, sun kai farmaki a kan wani tsibirin dake Tabkin Chadi, bayan da aka samu rahoton cewa ‘yan Boko Haram sun a hallara a wurin domin kai farmaki kan garuruwan dake kusa. An kasha ‘yan bindiga 7 a wannan farmakin, yayin da sauran suka gudu, wasu suka tsallaka cikin Jamhuriyar Nijar, wasu kuma Chadi.