Daya daga cikin muhimman sauye-sauyen da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Leftana-Janar Azubuike Ihejirika, ya amince da a yi, shi ne na sauya babban kwamanda mai kula da sabuwar runduna ta 7 da aka kirkiro kwanakin baya, wada kuma take da hedkwata a Maiduguri.
Wannan runduna it ace ta ke kula da yaki da tsageran Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Sanarwar da darektan hulda da jama’a mai barin gado na rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Ibrahim Attahiru, ya rattaba ma hannu, ta ce tsohon kwamanda (GOC) na runduna ta 7 a Maiduguri, Manjo-janar Obidah Ethan, yanzu shi ne ya zama hafsa mai kula da Harkokin da suka shafi soja da farar hula.
Manjo-Janar Junaid Bindawa, shi ne zai karbi ragamar kwamanda (GOC) mai kula da runduna ta 7 ta sojojin Najeriya mai yakar ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.
Sassan tsaro da dama a Najeriya sun ayyana tsammanin ganin irin wannan sauye-sauyen a saboda irin abubuwan da suke wakana a yankin arewa maso gabashin kasar.
A cikin ‘yan kwanakin nan, tsageran Boko Haram sun kai hare-hare a kan barikin sojoji na garin Bama, da kuma sansanin mayakan sama dake Maiduguri, abubuwan da suka nuna cewa har yanzu da sauran aiki a gaba wajen shawo kan wannan fada da ya koma na sari-ka-noke.