Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Kan Masu Bukin Aure a Jihar Borno


Rahotanni dsaga karamar hukumar Hawul sun ce 'yan bindiga biyu a kan babur suka bude wuta kan masu bukin suka kashe mutane 8.

Wasu 'yan bindiga biyu a kan babur, sun bude wuta a kan masu bukin aure a wani gari dake yankin kudancin Jihar Borno, suka kashe mutum 8, suka raunata wasu da dama.

Rahotannin dake fitowa daga yankin karamar hukumar Hawul na cewa wannan lamarin ya faru ne ranar asabar, a lokacin da 'yan'uwa da abokan arziki suka hallara domin taya ango da amarya murnar aurensu.

Kwatsam da misalin karfe 2:00 na rana, sai wasu 'yan bidniga biyu suka isa wannan wuri kan babur, kuma suka fara bude wutar kan mai uwa da wabi. Nan take mutanen 8 suka mutu a wurin.

An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci dabam-dabam dake yankin.

Kakakin shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya mai hedkwata a Maiduguri, Kanar Mohammed Dole, yace ba ya da masaniya game da wannan lamarin.

Babu wani bayanin da aka samu na wadanda suka kai harin, ko 'yan tsagera ne ko kuma wadanda suke yin gaba ne da ma'auratan.

An sha samun irin wannan harin a Jihar Borno, inda 'yan bindiga ke abkawa taron bukin aure, amma akasarin lokuta ba a sanin musabbabin haka da yake 'yan bindigar su na tserewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG