Wani mai magana da yawun ‘yan sandan, ASP Musa Magaji Majiya, yace an samu Hassan Zein lafiyarsa kalau, bayan da aka jefar da shi jumma’ar nan a wajen birnin Kano.
A ranar litinin ne wasu ‘yan bindiga suka abka cikin kamfanin Mr. Zein, M.C. Plastic Co, suka yi awon gaba da shi.
Iyalansa suka ce ba a nemi su biya kudin diyya ba, kuma bas u biya ba, koda yake an saba neman kudin diyya kafin a sako mutanen da aka sace a Najeriya. Shi ma jami’in ‘yan sanda ASP Majiya, yace ba a biya diyyar ko kwabo ba.
Yace ‘yan sanda sun a ci gaba da binciken wannan lamarin, kuma babu wanda aka kama dangane da satar Kwaran.