Kungiyar Niger Delta Avengers bayan ta fasa bututun man fetur a yankin ta kara da barzanar balle yankin daga tarayyar Najeriya.
Kungiyar ta kara da cewa nan ba da jimawa ba zata kaddamar da sabbbin takardun kudinta, da tutar kasa, da kuma taken kasa.
Amma hedkwatar tsaron Najeriya inji kakakinta Janar Rabe Abubakar yace idan abun ya zama dole sojin kasar zasu yi anfani da karfin tsiya su murkushe duk wanu yunkurin ballewa daga kasar.
Janar Abubakar yace sojojin Najeriya sun yadda da cewa Najeriya kasa daya ce kuma duk abun da zasu yi su tabbatar ta cigaba da kasancewa kasa daya zasu yi. Yace duk wani dake da nufin wargaza kasar to ya tabbata za'a murkusheshi da karfin da kundun tsarin mulkin kasa ya ba sojoji.
Masana harkokin tsaro irinsu Dr.Muhammad El-Nur Dengel yace yunkurin kungiyoyin IPOD da NDA barazana ce kawai. Yace da sukan yi barazana su samu kudin banza to yanzu babu kudin banza. Da akan nemesu a zauna dasu a kawo wasu kudade a basu amma duk wadannan sun kau. Idan akwai masu daure masu gindi hukumomin tsaro sun sansu kuma ya kamata a ja masu kunnuwa.
Kwararru irinsu Alhaji B. Abba na ganin al'amarin ta wata fuska daban. Yace maganar ballewa kowa ya san gudummawar da kowa ke bayarwa kuma wadanda suka san yadda aka yi yakin basasa ba zasu shiga irin wannan magana ba. Yakama su sani ba mai kadai kasar zata ci ba. Wadanda suke kawo barazanar wadanda da can suna cikin gwamnati amma abu ya birkice masu yanzu shi ya sa suka haukace.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5