Wata kungiyar 'yan tawaye ta Nigeria tayi watsi da tayin da gwamnati tayi mata na cewa a zo a zauna a tattauna don tsaida hare-haren da 'yan tawayen ke kaiwa kan butatan man fetur na kasar.
A yau Laraba ne kungiyar tsageran Niger delta da ake kira "Avengers" suka bada bayani a dandalinsu na Twitter inda suka ce su ba wani kwamitin gwamnati da suke wata tattaunawa da shi.
Kungiyar kuma ta tabattarda cewa lalle ta yi anfani da bam wajen tarwatsa wata rijiyar mai, mallakar kampanin Cheveron.
Kungiyar ta Avengers ta jima tana daukan alhakin kai hare-hare masu yawa akan rijijoyin mai da sauran kadarori mallakar kampunna irinsu Cheveron, Shell da ENI. Masana sun ce wadanan hare-haren sun janyo wa Nigeria asarar kashi 25 cikin 100 na yawan man da take samarwa.