Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Niger Delta Na Kara Kai Hare-hare


Mayakan tsagerun Niger Delta
Mayakan tsagerun Niger Delta

Rundunar sojojin ruwan Najeriya tace mayakan sa kai na tsagerun Niger Delta da aka sani da suna Niger Delta Avengers ko NDA sun zafafa kai hare-hare fiye da da can.

Shugaban tsare-tsare na rundunar Rear Admiral Jacob Ajani shi yayi karin haske kan karuwar hare-haren.

Yace bayanan leken asiri da muke dashi wanda ba zan iya fada a fili ba musamman a wannan lokacin sun nuna cewa akwai wasu dalilan da suka tursasa tsagerun zafafa kai hare-hare.

Yace sintirin da suke yi mai taken Operation Tsare Teku na cikin matakan da sojojin ruwan ke dauka.

Tsagerun suna fasa bututun cikin ruwa da wadanda ba cikin ruwa suke ba. Jacob Ajayi yace suna aiki tukuru tare da sauran jami'an tsaro saboda daukan matakin bai daya.

Chief Chike Ogoriba na daga cikin mutane shida da suka zauna da marigayi shugaba Umaru Yar'Adua har aka samar wa 'yan bingigan yankin Niger Delta ahuwa.

Dangane da matsalar yankin yanzu Chief Ogoriba yace baya jin akwai matsala, batun kawai shi ne yakamata shugaban kasa ya kaddamar da dokar ta baci ta raya yankin Niger Delta cikin gaggawa domin magance matsalolin da a can baya ba'a iya shawo kansu ba.

Masu sharhi na ganin gwamnatin tarayya ta samar da shirin ahuwa ga hukumar raya yankin Niger Delta da ma'aikata guda sukutun domin raya yankin.

Akan makudan kudin da ake ba yankin Chief Ogoriba yace shirin ahuwa da aka yiwa mayakan wanda akan ware masa kudi nera biliyan 60 zuwa 70 kowace shekara, a wannan shekarar nera biliyan 20 kacal aka ware. Ita ma ma'aikatar raya yankin dake samun kudi nera miliyan biyar aka ware mata kuma gina hanya kawai ka iya lakume biliyan dubu hudu. Yace banda haka ba'a sakewa 'yan asalin wurin mara.

Abdulmunmuni Gambari kwararre akan Niger Delta yace amma su shugabannin yankin sun ce wadanda gwamnati ke zama dasu basu sansu ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG