A taron wa’azi na kasa da kasa daya gudana a Bauchi, shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah, (JIBWIS), Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa tsarin siyasar karba-karba ya kawo nakasu wa tsarin mulki irin ta Dimokaradiya.
Shugaban Majalisar Malaman, Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir, yayi wannan furuci ne a hira da manema labarai a karshen taron wa’azin
Da aka tambayeshi game da batun tsaro a Najeriya, shugaban na Majalisar ta Malamai, ya danganta faruwan hakan kan kasashen ketare, da kuma wasu kabilu da basu son zaman lafiya a Najeriya.
Daga bisani Malamin, yayi addu’ar zaman lafiya a Najeriya da kuma baiwa shugabanni ikon gudanar da mulki mai adalci.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:
Your browser doesn’t support HTML5