Siriya Da Lebanon Za Su Kulla Sabuwar Alaka Bayan Sama Da Shekaru 20 Ba Sa Ga Maciji

Lebanon Syria

Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.

Sabon shugaban Syria da firaministan kasar Lebanon sun yi alkawarin kulla alaka mai dorewa a jiya Assabar, a ziyarar farko da wani shugaban gwamnatin Lebanon ya kai Damascus tun bayan yakin basasa a shekara ta 2011.

Ziyarar ta firaminista Najib Mikati ta zo ne bayan da 'yan tawayen da masu kishin Islama ke jagoranta, suka kwace ikon Damascus a watan da ya gabata, wanda ya kawo karshen mulkin shugaba Bashar al-Assad.

Gwamnatocin baya na Lebanon sun kaurace wa ziyartar kasar Siriya, a daidai lokacin da ake zaman dar-dar na cikin gida, dangane da goyon bayan kungiyar mayakan Hizbullah ga Assad a lokacin rikicin.

Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.

Ya ce lokaci ya yi da za a bai wa al'ummar Siriya da Lebanon damar kulla kyakkyawar alaka, yana mai fatan shugabancin Joseph Aoun zai kawo zaman lafiya a Lebanon.

Sharaa ya ce sabuwar Siriya za ta yi "alaka iri daya da kowane bangare" a Lebanon, kuma za ta "yi kokarin shawo kan matsalolin ta hanyar tattaunawa da sulhu."