"Da bakin ciki muka sanar da rasuwar masoyiyarmu Sinead. 'Yan uwanta da abokanta sun yi matukar bakin ciki kuma sun nemi a ba su sirri a wannan mawuyacin halin da su ke ciki," in ji RTE a wata sanarwa daga dangin mawakiyar.
Har yanzu dai ba a a san sanadiyar mutuwarta ba.
Ta shahara sosai ne saboda ra'ayoyinta na zahiri game da addini, jima'i, goyon bayan ‘yancin mata da kuma yake-yake.
An haifi Sinead Marie Bernadette O'Connor a wata unguwar masu arziki a Dublin, a ranar 8 ga Disamba, 1966. A cikin tarihinta na 2021, O'Connor ta ce mahaifiyarta, wacce ta mutu a wani hatsarin mota a 1985, ta ci zarafinta da ta ke yarinya..
Sinead, wadda ta yi aure sau hudu, kuma wadda aka nada ta a matsayin limamiyar coci a shekarar 1999 ta wata kungiyar Katolika da ta balle ta musulunta a shekarar 2018 inda ta canza sunanta zuwa Shuhada Sadaqat, duk da cewa ta ci gaba da yin waka da sunan Sinead O'Connor.