Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kun San Abu Na Karshe Da TB Joshua Ya Fada Kafin Rasuwarsa?


Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00

Marigayi TB Joshua.

An haifi TB Joshua a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1963 – ya rasu kwana shida kafin ya cika shekara 58.

Fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya mai mabiya a sassan duniya TB Joshua ya rasu.

Ya rasu yana da shekara 57 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin kasar.

“Allah ya karbi bawansa, TB Joshua.” Wata sanarwa da Cocinsa ta 'The Synagogue, Church of All Nations' ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce.

Sai dai sanarwar ba ta fadi musabbabi ko lokacin da shahararren mai wa’azin ya rasu ba, wanda asalin sunansa Temitope Balogun Joshua.

"A ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, 2021, TB Joshua ya yi jawabi a wajen taron da aka shirya don tattaunawa kan shirin gidan talbaijin na Emmanuel.”

Marigayin na da fitaccen gidan talabijin da yake wa’azi, wanda ake kira Emmanuel TV.

A cewar sanarwar, abu na karshe da malamin addinin Kiristan ya fada shi ne, “ku sa ido, ku yi addu’a.”

Tun a ranar Asabar jita-jitar mutuwar mai wa'azin ta karade shafukan sada zumunta.

Karin bayani akan: TB Joshua, Church of All Nations, Kiristan, Nigeria, da Najeriya.

Wani abu da ya sa TB Joshua yin fice a duniya shi ne, ikirarin da ya yi, na cewa yana iya warkar da cututtuka iri-iri, ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS.

Hakan ya sa jama’a daga sassan duniya, kan yi tattaki har zuwa Najeriya don neman waraka.

Kazalika, kamar yadda rahotanni ke nunawa, TB Joshua, malami ne dake ikirarin iya hangen abin da zai faru a gaba, lamarin da ya jima yana janyo ka-ce-na-ce.

Katafaren ginin Mujami'arsa da ke Legas ya taba ruftawa a shekarar 2014, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 100 ciki har da ‘yan kasar Afirka Kudu da dama.

An haifi TB Joshua a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1963 – ya rasu kwana shida kafin ya cika shekara 58.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG