Shugaban yankin Catalonia na kasar Spain, Carles Puihdemont na dab da gabatar da jawabi gaban wakilan Majalisar yankin a yau Talata, a yayinda gwamnatin kasar Spain, ke nuna damuwar kila wakilan Catalan su jefa kuri’ar ayyana 'yancin cin gashin kan yankin.
WASHINGTON D.C. —
Shugabanin siyasa a Spain da wasu kasashen waje, jiya Litinin suka yi kira ga shugabanin Catalonia da kada su ayyana yancin cin gashi kai domin sassauta zaman tankiya a kasar.
Shima shugaban babar jam’iyar masu hamaiya ta kasar Spain, shugaban yan gurguza Pedro Sanchez, yayi kira ga shugabanin Catalonia, da su yi watsi da yunkurin ayyana 'yancin cin gashin kai.
Jiya Litinin Kasashen Jamus da Faransa, suma suka yi nazari akan balewar, Shugabar Jamus Angela Merkel, ta jaddada goyon bayan ta, ga hadin kan kasar Spain, kuma tayi kira ayi tattaunawa tsakanin bangarorin kasar Spain.
Shugaba Catalonia bai bayana abinda jawabin nasa zai kunsa ba.