Musulmi ‘yan kabilar Rohingya su akalla 12 ne suka mutu cikin ruwa a lokacin da kwale-kwalensu dake shake da mutane ya kife jiya lahadi da dare, a lokacin da suke tserewa daga Myanmar don neman mafaka a kasar Bangladesh.
Kwale-kwalen ya nutse a kogin Naf wanda ya raba kasar Myanmar da Bangladesh.
Wani jami’in bakin iyaka na Bangladesh ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa gawarwakin 12 sun hada da na yara 10 da wata tsohuwa da kuma wani magidanci. Yayi hasashen cewa tun da kwale-kwalen ya kife a kusa da Myanmar ne, watakila wasu daga cikin fasinjojin sun iya sun yi ninkaya zuwa bakin gaba.
Jami’ai basu san adadin mutanen dake cikin kwale-kwalen a lokacin da ya nutse ba, amma kuma a yawancin lokuta ana diban mutane fiye da kima cikin irin wannan kwale-kwale.
Daga watan Agusta zuwa yanzu, fiye da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya su rabin miliyan daya sun gudu daga Jihar Rakhine ta Myanmar zuwa Bangladesh
Facebook Forum