Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Koriya ta Arewa Yace Nukiliyar Kasar Ta Yiwa Kasashen dake Takalarsa Kashedi Ne


Kim Jong Un, shugaban kasar Koriya ta Arewa
Kim Jong Un, shugaban kasar Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa ya ci gaba da shirin makamin nukiliyar kasarsa duk da takura wa gwamnatinsa da kasashen Amurka da Japan keyi

: Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un, na cigaba da nuna bijirewa, ta wajen bayyana shirin makamin nukiliyar kasarsa da cewa wani "takobi mai daraja," ne na kare kasar daga takala, duk kuwa da cigaba da takura wa gwamnatinsa da Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Japan Shinzo Abe ke yi.

Kafar labaran gwamnatin Koriya Ta Arewa ta bayyana cewa ranar Asabar Kim ya gaya ma mashahurin kwamitin nan na jam'iyyar ma'aikata mai mulki cewa makaman nukiliya din makari ne mai tabbatar ma kasar diyaucinta daga abin da ya kira "dadaddiyar barazanar makaman nukiliya daga kasar Amurka mai son danne wasu kasashen."

To amma ya amsa cewa rikicin Koriya Ta Arewa da Amurka, da Japan da Koriya Ta Kudu da wasu kasashen game da shirinta na nukiliya matsala ce mai sarkakkiya a matakin kasa da kasa.

Jaddada goyon baya ga shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa da Shugaba Kim ya yi, ya faru ne bayan da Shugaba Trump ya fadi ranar Asabar cewa "abu guda ne kadai maganin wannan rigimar da ake yi da Koriya Ta Arewa" ganin yadda gwamnatocin Amurka da su ka shude su ka yi ta tattaunawa da Koriya Ta Arewar ba tare da cimma komai ba.

Ba a san takamaiman abin da Trump ke nufi da wannan maganar ba, to amma wasu na ganin kamar dai matakin soja ya ke nufi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG