Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Na Matsa wa Shugabannin Catalonia Su Yi Watsi da Yunkurin Ballewa daga Spain


Shugaban Yankin Catalonia a Spain Charles Puigdemont
Shugaban Yankin Catalonia a Spain Charles Puigdemont

Wasu kasashen duniya da wasu shugabanni cikin kasar Spain suna matsa wa shugabannin yankin Catalonia lamba su yi watsi da shirin ballewa daga kasar Spain a daidai lokacin da Charles Puigdemont ke shirin yin jawabi a majalisar dokokin yankin

Shugabannin yankin Catalonia na fuskantar karin matsin lamba daga gida da kasashen waje kan cewa su watsar da shirinsu na ayyana cin gashin kai daga Spain, gabannin jawabin shugaban yankin da aka shirya yi.

A yau Talata ne aka shirya shugaban yankin Carles Puigdemont, zai yi jawabi gaban ‘yan majalisar dokokin yankin nasa, hakan yasa gwamnatin Spain ta shiga damuwa da tsoron kada ‘yan majalisar su kada kuri’ar yarda da yunkurin neman yancin kan.

A kan hakan ne, shugabannin siyasa na ciki da wajen kasar jiya Litinin suke kira ga shugabannin Catalan da su dakatar da shirinsu don samar da zaman lafiya a kasa baki daya.

Magajiyar Garin birnin Barcelona itace wadda tayi magana a baya-bayannan inda ta nuna rashin goyon bayanta da rabuwar kasar, tana mai cewa hakan zai iya saka al’umma cikin wani hali. Ada Colau, tayi kira ga duk bangarorin da wannan lamari ya shafa da su zauna don samo hanyar warware matsalar da ba taba ganin irinta a tarihin dimokaradiyyar Spain ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG