Hakan ya biyo bayan ayyana sunayen mutane biyu da kwamitin Farfesa Ango Abdulahi, kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa ya gudana a garin Minna na Jihar Neja, da aka ce gwamnan Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed da kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Senata Bukola Saraki.
Kamar yadda bincike ya nuna mutane hudu masu son yin takarar kujerar shugabancin kasa a jam’iyar PDP da suka hada da, gwaman Sokoto, Aminu Tambuwal, da Alhaji Aminu Hayatu-Deen, da Bala Abdulkadir Muhammed, gwamnan Bauchi, da kuma Senata Bukola Saraki sun amince da fidda dan taka guda daga cikinsu, amma da sakamako ya fito sai aka samu canjin ra’ayi.
Dokta Ladan Salihu, dan jam’iyar PDP ne kuma ya halarci wajen taron da aka gudanar a garin Minna, yayi fashin baki kan batun jeka ka dawo da ake yi. Ya ce ya kamata su samu hadin kai.
Ku Duba Wannan Ma Tasirin Saya Wa ‘Yan Siyasa Fom Din Neman Tsayawa Takara A Zaben 2023Mallam Dogo B B, shi ya jagoranci zaman taron Dattawan Jam’iyar PDP din da aka gudanar a Bauchi ya bukaci ganin uwar jam’iyar PDP din data gayyaci duk ‘yan takaran don neman maslaha.
Madam Hauwa Aliyu, daga jihar Yobe, ta amince da sakamakon kwamitin farfesa Ango Abdullahi, sai dai tana goyon bayan takarar, wamnan Bauchi Senata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:
Your browser doesn’t support HTML5