Shugabannin Kungiyar Kasashen G7 Sun Amince Da Shirin Biden Na Tsagaita Wuta A Gaza

G7

Shugabannin kungiyar kasashe bakwai na G7 masu karfin dimokuradiyya "sun amince da tsagaita bude wuta da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su a yakin Gaza, yarjejeniyar da shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana tare da yin kira ga Hamas da ta amince da shi."

WASHINGTON, D. C. - Yarjejeniyar za ta haifar da tsagaita bude wuta nan take a Gaza, da sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, da bude hanyar karo taimakon jinkai don rarrabawa a fadin Gaza, da kuma kawo karshen rikicin, tare da tabbatar da muradun tsaron Isra'ila da tsaron fararen hula na Gaza, a cewar sanarwar.

Kungiyar ta G7, wadda Italiya ke rike da shugabancin karba-karba na shekarar 2024, ta sake jaddada goyon bayanta ga "sahihiyar hanyar samar da zaman lafiya da za ta kai ga kafa kasashe guda biyu."

Biden ya gabatar da abin da ya bayyana a matsayin shawarwarin tsagaita bude wuta na Isra'ila mai matakai uku a makon da ya gabata, inda ya samu kyakkyawar amsa ta farko daga Hamas.

Wani mataimaki ga firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa Isra'ila ta amince da tsarin da aka cimma na dakile yakin Gaza, ko da yake ya bayyana shi a matsayin mara kyau ga Isra’ila da kuma bukatar karin aiki.

Sanarwar ta kungiyar G7 ta ce "Muna kira ga Hamas da ta amince da wannan yarjejeniya, cewa Isra'ila a shirye take ta ci gaba da kasancewa tare da ita, kuma muna kira ga kasashen da ke da tasiri kan Hamas da su taimaka wajen ganin ta yi hakan."

-Reuters