Shugabannin kasashen Turai suna birnin Brussels, suna gudanar da wani muhimmin taron da zai shata makomar takardar kuddinsu ta Euro.
Wasu jami’ai sun bayyana wannan taron da cewa shine dama ta karshe ta warware matsalolin dake addabar takardar kudin ta Euro, wacce dimbin bashin da ake bin kasashen Turan ke janyo mata ci-baya.
Sai dai kuma, tun ma kafin a soma taron aka fara samun sabanin ra’ayi a tsakanin mahalartansa akan yadda za’a tinkari wannan matsalar ta bashi wacce ke barazana ga tattalin arzikin duniya baki dayansa.
Yanzu haka, sha’anin tattalin arzikin kasashen turai sha bakwai dake anfani da wannan takardar kudin ta Euro, ya ja ya tsaya cik, har wasu sun fara hasashen cewa wannan na iya janyo tabarbarewar tattalin arzikin wasu daga cikin kasashen.
Domin magance wannan al’amarin ne yassa shugabar kasar Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy suka fito suna kira akan ‘yan’uwansu kasashen Turai da su rage yawan kudaden da suke kashewa.