Shugabannin kasashen gabashin Afirka na yabawa da kashe Usama bin Laden, wanda rassan kungiyarsa ta al-Ka’ida ta ke ta kai kawo a yankin nasu.
Shugaban Kenya Mwai Kibaki ya fadi jiya Litini cewa kashe bin Laden wani adalci ne ga wadanda harin da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka da ke Nairobi ya rutsa da su.
Al-Kai’da ta yi ikirarin kai wannan harin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 212, da kuma harin da aka kai rana guda kan ofishin jakadancin Amurka a Tanzania, wanda ya yi sanadin mutuwar karin mutane 11.
Firayim Minista Raila Odinga ya fadi jiya Litini cewa mutanen Kenya sun yi marhabin da kashe bin Laden to amman sai ya yi gargadin cewa kisansa bai kawo karshen yaki da ta’addanci ba.
A kasar Uganda, wani mai magana da yawun gwamnati ya bayyana kashe bin Laden da cewa wani muhimmin al’amari ne sannan ya ce dakarun Uganda da ke Somalia za su cigaba da yaki da mukarraban al-Ka’ida wato mayakan al-Shabab.
Firayim Ministan Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed ya gaya wa Muryar Amurka, Sashen Harshen Somalia, cewa gwamnatinsu ma ta yi marhabin da kisan to amman tana shirin tarar yiwuwar ramuwar gayya daga daruruwan ‘yan al-Ka’ida da ke harkokinsu a kasar.
Firayim Ministan ya yi ta amfani da kalaman tsawatawa kan bin Laden, ya na mai cewa ya sa an dauki addinin Islama a matsayin addinin tashin hankali, sannan ya ce ita kanta Somalia na fama da aika-aikar al-Ka’ida da ta’addanci.