Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta a Pakistan Bayan Mutuwar Bin Ladin

Zanen gidan da aka kashe Osama bin Laden a ciki a Pakistan kenan.
Zanen gidan da aka kashe Osama bin Laden a ciki a Pakistan kenan.

Amurka ta daina ayyukan yau da kullum a ofishin jakadancinta da wasu gine-ginen diflomasiyya uku da ke Pakistan, har sai yadda hali ya yi, kwana guda da kashe Osama bin Laden da dakarun Amurka su ka yi, a birnin Abbottabad na kasar Pakistan.

Ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Islamabad, ya bayar da sanarwar cewa, ya dakatar da ayyukan yau da kullum da su ka shafi jama’a, amman har yanzu za a iya hidima ta gaggawa ga ‘yan asalin Amurka. Sanarwar ta ce gine-ginen jakadancin da ke Peshawar, da Lahore da Karachi, su ma an rufe su zuwa wani lokaci.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta gargadi Amurkawan da ke kasashen waje, cewa su kula sosai, a sa’ilinda ake fargabar yiwuwar fuskantar ramuwar gayyar mutuwar shugaban al-Ka’ida. Sanarwar ta ce duk wata kadarar Amurka da ke fadin duniyar nan ta shiga shirin ko ta kwana, kuma tana iya daina hidima ga jama’a na wucin gadi ko kuma ta dakatar da harkokinta saboda batun tsaro.

A halin da ake ciki kuma Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta ce yakin da ake yi da al-Kaida da mukarrabanta, bai zo ga karshe saboda mutuwar Osama bin Laden ba.

Clinton ta ce Amurka za ta cigaba da sa kafar wando guda da duk masu kashe wadanda bas u jib a basu gani ba.

XS
SM
MD
LG