Shugabannin Kasashen ECOWAS Sun Kasa Cimma Matsaya A Taron Da Suka Yi A Ghana

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

Shugabannin sun kasa yanke hukunci akan matakin da ya da dace da kasashen da suka yi juyin mulki a yankin Afrika ta yamma.

ACCRA, GHANA - Ranar Asabar 4 ga watan Yuni ne shugabannin na kasashen ECOWAS suka tattaru a Accra babban birnin kasar Ghana don tattauna matakan da suka dace mambobin kasashen su dauka domin ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Guinea, amma basu iya cimma matsaya ba. A saboda haka suka dage zaman taron zuwa watan Yuli mai zuwa domin ci gaba da duban lamarin.

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

Wanda ya jagoranci taron shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya bayyana cewa taron zai ci gaba da maida hankali akan rikicin siyasa a yankin Afrika ta yamma da juyin mulkin da aka yi tun daga shekarar 2020.

"Muna da kyakkyawan zato za a iya kawo karashen matsalolin, a cewar Addo. Burin mu shi ne mu samar da hanyoyin maida kasashen da ke fama da juyin mulki komawa tafarkin dimokradiyya." Wannan zai taimaka wa kasashen su iya magance matsalolin tsaro da sauran kalubale da suke fuskanta.

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

Bayan tafka mahawara tsakaninsu, shugabannin sun kasa cimma matsaya akan matakin da ya dace a dauka akan kasar Mali, wadda ta ki gabatar da shirin mika mulki ga farar hula da kuma katse hulda da ta yi da kungiyar G5 Sahel da ke yaki da ‘yan ta’adda.

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

Mallam Adib Sani, mai sharhi kan harkar tsaron ciki da wajen Ghana, ya ce kungiyar ECOWAS ta nuna gazawa saboda ba ta iya magance wasu matsaloli da suka shafi yankin ba musamman batun tsaro da rashin ayyukan yi ga matasa, da sauransu.

Tuni dai takunkumin da aka kakabawa kasashen da suka yi juyin mulkin ke tasiri akan tattalin arzikinsu da ma na yankin Afrika ta yamma.

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

Sai dai malam Imran Hashiru Dikeni masani a fannin tattalin arziki, ya ce takunkumin da aka sanya wa kasashen zai kara fadada gibin da ke tsakanin talakawa da masu hannu da shuni.

Rahoton da majalisar dinkin duniya ta gabatar a baya bayan nan ya ce takunkumin da aka sanya wa wasu kasashen yammacin Afrika na daga cikin abubuwan da suka janyo kuncin rayuwa a yankin.

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS A Ghana

saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Kasashen ECOWAS Sun Kasa Cimma Matsaya A Taron Da Suka Yi A Ghana