Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Gudanar Da Taro Game Da Takunkumin Da Aka Saka Wa Mali


Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo Addo

Shugaban Kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo Addo, shi ne wanda ya bude taron Kungiyar Tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka wato ECOWAS da aka gudanar a birnin Accra na Ghana, inda ya ke cewar taron ya karkata ne akan kasashe uku da suka fuskanci juyin mulki.

Shugaban Kungiyar ECOWAS, Jean Claude, ya ce Kungiyar ta ECOWAS ta amince da bai wa Asimi Gaita, wanda ya jagoranci juyin mulki a kasar Mali, watanni 24 kamar yadda suka nema, domin kasar ta tsayar lokacin zabe wanda da hakan ECOWAS za ta janye takunkumin da aka kakkaba musu.

Mallam Irbad Ibrahim, masani a harkokin tsaro, ya ce abin da ya kamata Kungiyar ECOWAS ta yi wannan lokacin shi ne, ta dauke takunkumin da ta dora wa kasar Mali. Ya kara da cewa shugabannin Kungiyar ECOWAS su yi duba da wasu kasashen da shugabanni su ke tafiyar da harkokin mulkinsu ba daidai ba, saboda a cikin tsarin ECOWAS ba ta da 'yancin ta saka baki a wasu harkokin mambobin cikin gida.

Mallam Irbad ya ce me ECOWAS za ta fadi game da yanda ake tafiyar da mulki a kasar Togo? A karshe ya ce har yanzu ECOWAS dai ba ta cimma manufa ba da ake so ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG