Shugabannin Dakarun Sojan Kasashen Kungiyar ECOWAS Sunyi Taron Karfafa Tsaro  a Accra

Shugabannin Dakarun Sojan Kasashen Kungiyar ECOWAS.

Taron wuni biyu na shugabannin dakarun tsaron kasashe goma sha hudu karkashin kungiyar ECOWAS da aka gudanar a Accra ya maida hankali bisa matakan shawon kan iftila'in da ya ritsa da wasu mambobin kungiyar.

Wato hare hare masu nasaba da ta'addanci da yayi sanadiyar mutuwar mutani fiyeda dubu goma sha shidda da dari bakwai da ashirin da shidda a yankin cikin shaikara uku.

Yayin jawabinsa ministan harkokin tsaron kasar Ghana, Dominic Nitiwul da ya karbi bakwancin shugabannin dakarun tsaron kasashen a Accra yace hare haren ta'addanci fiye da dubu biyar da dari uku ne yan ta'adda suka kai a wasu kasashen Afrika ta yamma. Abinda ya tilatsa miliyoyin al'uman yankin ficewa matsugunansu.

Ministan na bukatar da shugabannin dakarun tsaron kasashen su hada karfi karfe gurin yin musanyan bayanan sirri tsakaninsu domin karfafa tsaron yankin.

ECOWAS

To sai dai ya kara da cewa kamata yayi da shugabannin tsaron suyi watsi da kabilanci ko wata al'ada ko wani addini dama yare domin ganin sun cimma manufofinsu na samarda tsaro da zaman lafiya.

Ministan tsaron Ghana ya jadadda muhimmanci bai wa falaren hula damar fitarda shugaban kasa a kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS tareda gudunmuwa mai yawan gaske da shugabannin tsaron kasashen zasu bayar gurin samarda tsaro tare da zaman lafiya.

Ku Duba Wannan Ma ECOWAS Ta Yi Watsi Da Wa'adin Mulkin Shekara Biyar Da Sojojin Mali Ke Son Yi

Rtd Umar Sanda tsohon jakadan Ghana a kasar Masar kana tsohon shugaban musulman dakarun soja a Ghana yace wannan taro ya taimaka sosai musamman musanyan bayanan sirri tsakanin kasashen domin tabbatarda tsaron yankin.

To sai dai wani abinda ya kuma dau hankullan jama'a bisa wannan taron shine wasu kasashen da aka kakabawa takunkumai sakamakon kifarda gwamnatotinsu wato Guinea da Mali da Burkina Faso duk sun halarta, abinda mai sharhi bisa harkar tsaro Mallam Irbad Ibrahim yace matakin gayyatansu da Ecowas din tayi ya dace sosai.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Dakarun Sojan Kasashen Kungiyar ECOWAS Sunyi Taron Karfafa Tsaro  a Accra