Jiya Lahadi Shugaba Obama da takwaransa na Rasha Putin sun cimma daidaito akan bukatar yin sauyin harkokin siyasa a kasar Syria.
Shugabannin biyu sun amince da bukatar aiwatar da shirin a karkashin jagorancin 'yan Syria tare da Majalisar Dinkin Duniya wadda zata shiga tsakani da kuma tsagaita bude wuta domin a kawo karshen yakin basasan da yaki ci ya ki cinyewa cikin shekaru hudun da suka yi suna fafatawa.
A taron G-20, wato taron kasashen da suka fi karfin masana'antu da tattalin arziki, shugabannin suka hadu har suka samu ganawar mintuna talatin.
Inji Fadar White a ganawar ta shugabannin sun yi shawarwari masu ma'ana da ka iya yin tasiri a yanayin da Syria ke ciki. Haka ma mai ba shugaba Putin shawara a harkokin da suka jibanci kasashen waje ya ce shugabannin biyu sun yi shawarwari masu zurfin gaske.
Wani jami'in Fadar White House yace shugabannin biyu sun yi la'akari da cigaban da aka samu ta tafuskar diflomasiya a shawarwarin da ake yi a Vienna.
Daga karshe Shugaban Amurka Barack Obama ya yi maraba da yunkurin wasu kasashen duniya keyi na murkushe kungiyar ISIS a Syria da ma kakkabesu daga koina a duniya. Haka ma sojojin Rasha sun maida hankalinsu akan yakar ISIS.