Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawancin Hare-haren Rasha a Syria Tana Aunawa ne Kan 'Yan Tawaye Masu Sassaucin Ra'ayi


Shugaban Rasha Putin (a dama) da shugaban Syria al-Assad (a hagu)
Shugaban Rasha Putin (a dama) da shugaban Syria al-Assad (a hagu)

Manyan jami'an difilomasiyya na Amurka sun ce kashi 85-90 na hare haren da Rasha take kaiwa da jiragen yaki a Syria sun afkawa kungiyoyi 'yan tawayen kasar masu sassaucin ra'yi, ba kungiyar ISIS ba.

Mukaddasan sakataren harkokin wajen Amurka Anne Patterson da Victoria Nuland ne suka fadi haka lokacinda suke bada shaida a gaban kwamitin kula da harkokin waje a majalisar dokokin kasar.

A gefe daya kuma, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka da ake kira "Pentagon" Kanal Steve Warren, ya gayawa manema labarai cewa kasa da kashi 10 cikin dari na farmakin da Rasha take kaiwa da jiragen yaki ne take auna su kan kungiyar mayakan sakai ta ISIS.

Amma jami'an sojoji dana difilomasiyyar Rasha duk sun dage cewa ISIS suke auna hare hare da kasar take kaiwa.

A zaman na jiya Laraba shugaban kwamitin Ed Royce yace Rasha ta dauki mataki na kai tsaye wajen "juya makomar Syria nan gaba" amma ba akan turba mai kyau ba."

Mukaddashiyar sakataren harkokin wajen na Amurka Victoria Nuland tace, "Rasha tana dan-dana kudarta" a yunkurin karfafa mulkin al-Assad. Ta lura cewa Rasha tana kashe abunda ya kama daga dala milyan $2 zuwa 4 ko wace rana domin tafiyar da matakin sojin da take dauka a Syria. Ta kara d a cewa idan Rasha ta zabi wannan matakin fiyeda bukatun jama'arta, zata iya ci gaba da yin haka na lokaci mai tsawo.

XS
SM
MD
LG