Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Rasha Ya Bukaci A Tantance Bangarorin Da Za Su Tattauna


A yau Laraba, Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergie Lavrov, ya nuna bukatar a tantance bangarorin da za su shiga tattaunawar samar da maslaha kan rikicikn Syria da kua bangaren da za a rika kallo a matsayin ‘yan tawaye.

Lavrov ya furta wadannan kalamai ne yayin wani taron manema labarai, bayan wani taro da aka yi a Moscow da Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Staffan de Mistura, domin ganawa kan yadda za kawo karshen rikicin Syria a siyasance.

Rikicin na Syria dai ya halaka sama da mutane dubu 240 tun da ya barke a shekarar 2011.

A baya,ofishin shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce, sun ce shugaban ya gana da shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ta wayar talho, kuma dukkanin a shirye suke su ci gaba da tattaunawa.

De Mistura da Lavrov na cikin tawagar da ta tattauna a makon da ya gabata a birnin Vienna, wanda ya yi kira ga Majalisar Dinkin Dunbiya da ta kawo duk bangarorin da ke takaddama zuwa ka teburin tattaunawa.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG