Yayinda Trump ke ta kare kudurinsa na tasa kyeyar bakin haure zuwa kasashensu na asali, shi kuwa Trudeau yana cewa, 'yan gudun hijrar Siriya sun samu kwanciyar hankali a kasarsa.
Trudeau ya marabci 'yan gudun hijirar Siriya wajen 40,000 a Canada, a daidai lokacin da shi kuma Trump ya dakatar da shigowar 'yan gudun hijirar Siriyan, har sai illa masha'allahu, wanda wani bangare ne na shirinsa na takaita shigowar mutane daga wasu kasashe 7 masu rinjayen Musulmi, wadanda kasashe ne da ke fama da matsalar ta'addanci.
Da aka tambaye shi ko yana ganin idan 'yan gudun hijirar Siriya su ka zauna a Canada, bangaren arewa na kan iyakar Amurka zai kasance da cikakken tsaro, sai Trump ya ce, "Ai ba a kasancewa da kwarin gwuiwa dari-bisa-dari a al'amari irin wannan ba."
To amma bayan da aka fara kai samame kan bakin haure a 'yan kwanakin nan da zummar tasa kyeyar wadanda su ka aikata manyan laifuka, sabon Shugaban na Amurka ya yi shelar cewa, "Za mu fitar da su. Abin da na yi alkawarin zanyi ne kawai fa na keyi."
"Mu na kan damke miyagun, da masu safarar muggan kwayoyi .... mu na ta kakkama fitsararrun..." a cewar Trump, wanda ya kara da cewa, "Nan gaba jama'a za su yi farinciki matuka, i, farinciki matuka."
To amma Trudeau ya ce 'yan Siriya da su ka shiga Canada na "samun cigaba," kuma kawayen Canada sun fahimci dalilin Canada na marabtar 'yan gudun hijira daga kasashen da yaki ya daidaita.