Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Kin Jinin Kudurin Donald Trump a Mexico


Dubban mutane suka yi dafifi a kimanin manyan biranen kasar Mexico ishirin jiya Lahadi domin yin Allah wadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na gina ganuwa kan iyakar kasashen.

Jami’an kasar Mexico sun yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu talatin ne suka yi jerin gwano a biranen kasar biyu mafiya gima, Mexico city, da kuma babban birnin kasar Guadalajara.

Masu gangamin sun rike tutar kasar da kuma kwalaye dake bakanta Trump, da aka yi rubutu da turanci da kuma spaniyanci.

Bari gwamnatin Trump ta sani cewa, ba zamu mika wuya bori ya hau ba. Kasar Mexico bata taba mika wuya ba. A nan muna da jarumawa wadanda suka san ya kamata, da kuma sanin bukatar rungumar kowa. A nan ina ganin yara da manya, matasa da dattawa. Wannan yana nufin kasar Mexico zata ci gaba.

Masu zanga zangar sun kuma kushewa shugaban kasarsu Enrique Pena Nierto da suka ce, shugaban jeka-na-yika ne, wanda a ganin idonsa ake fama da kazamin cin hanci da rashawa da kuma tashe tashen hankali a kasar.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG