Wadanda aka zanta dasu sun ce abun da kasar ta gada shi ne mutane su fito su nuna kin amincewarsu da duk wani mataki da gwamnatin Amurka ta dauka.
Sunce sun fito ne yin zanga zangar duk da mugun sanyin da aka yi jiya amma sabo da kishin musulunci da kuma yadda Shugaba Trump ya ware musulmi akan cewa su ne 'yan ta'ada.
Wadanda suka yi magana sun ce addinin musulunci addini ne na zaman lafiya kuma tunda suke kasar basu taba tada hankalin kowa ba.
Zanga zangar ta hada da mutane daga kasashe dama musamman na yankin Afirka kuma hadda wadanda ma ba musulmi ba sun fito su nuna adawarsu.
Macin da musulmin suka yi a Bronx ya kammala da gangami a farfajiyar kotun tarayya tare da yin kira kowa ya dage da neman yancinsa.
Ruwan sama da aka yi da kankara basu hana mutane fitowa macin ba. Ahmed Gum na kungiyar Muslim Foundation of Amurka yana cikin wadanda suka yi jawabi a wurin macin. Yace zasu cigaba da matsawa shugaba Trump lamba har sai ya canza matsayinsa akan musulmi da baki.
Ga rahoton Yakubu Baba Makeri da karin bayani.