Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Duba Yadda Zai Tunkari Hukunci Kotu Akan Hana Wasu Shigowa Kasar


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Wani hadimin shugaban Amurka Donald Trump, ya fada jiya Lahadi cewa fadar White House tana duba "dukkan zabi da take da shi" a yunkurin tunkarar hukuncin da kotu ta zartas na dakatar da aiki da dokar shugaban kasa, wacce ta hana 'yan wasu kasashe bakwai da galibin mutan kasashen musulmi ne zuwa Amurka.

Babban mai baiwa shugaban Amurka shawara kan manufifin gwamnati Stephen Miller, yace gwamnatin Trump mai mako uku kacal, "tana nazatin ko wani mataki da take da shi, wajen ganin ta kare Amurka daga ta'addanci." Hadimin na shugaban kasa dan shekaru 31 da haifuwa ya gayawa shirin "Meet the Press na tashar talabijin ta NBC cewa, shugaban na Amurka yanada 'yanci ko hakkin yanke shawarar kan wadanda zai kyale su shigo Amurka,kuma jami'ai sun zabi wadannan kasashe bakwai ne bisa nazarin barazanar da ake fuskanta yanzu da kuma nan gaba."

Ahalinda ake ciki kuma hukumomin shige da fice na Amurka sun kama daruruwan bakin haure wadanda suke zaune a Amurka ba bisa ka'ida ba, a somame da suka kai a duk fadin kasar nan cikin makon jiya,kodashike hukumomi suka ce matakin bashi da wata nasaba da dokar da shugaban kasa da Mr. Trump ya sanya hanu akanta.

Da yake magana kan samamen ta shafinsa na Twitter jiya Lahadi, shugaba Trump yace "mataki kan bakin haure bata gari, cika alkawarin yakin neman zaben da nayi ne. 'Yan banga, da masu fataucin miyagun kwayoyi da wasu ana tusa keyarsu."

XS
SM
MD
LG