Shugaban Tanzania Na Tababa Kan Ingancin Rigakafin Coronavirus

A daidai lokacin da manyan kasashen duniya suka fara samar da allurar rigakafin cutar coronavirus, shugaban kasar Tanzania na tababa kan ingancin rigakafin.

Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli, ya gargadi Ministan Lafiyar shi da cewar, kada ya yi saurin karbar allurar rigakafin annobar coronavirus, yana mai cewar babu tabbacin rigakafin na da inganci ko kuma yana aiki.

A lokacin wani jawabinsa jiya Laraba a yammacin kasar, Magufuli, ya nuna tababa ko rashin amincewa da magungunan da kasashen Turai suka hada.

Ya kara da cewar “Idan har Turawa suna iya samar da magani, ai da suna samar da magungunan cutar Kanjamau da tarin fuka, da sun zama tarihi, haka da an samar da maganin zazzabin cizon sauro da ciwon daji.”

Magufuli, ya ummurci Ma’aikatar Lafiya da cewar kada su fara amfani da maganin har sai kwararru a kasar ta Tanzaniya sun tabbatar da ingancin rigakafin.

Ya ce Tanzania, ba zata zama kasar da za a yi gwajin allurar da ita ba.

Shugaban dai ya ayyana kasar da cewar basu da annobar coronavirus babu kuma wanda ya mutu sanadiyyar kamuwa da cutar.