Adadin masu kamuwa da cutar COVID -19 a fadin duniya na kusantar miliyan 100. Da safiyar yau Asabar Jami’ar Johns Hopkin ta sanar da cewa sama da mutane miliyan 98 suka kamu da cutar a duniya kuma an sami mace-mace sama da miliyan 2.
“A halin da ake ciki, har yanzu cutar na yaduwa, amma muma muna da abubuwa biyu da zasu taimaka: riga kafi da raguwar yanayin sanyi." Abinda Yves Van Laethema, mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar Belgium ya fada kenan game da cutar COVID-19 a kasar.
Mr. Yves ya ce ya na fatan yanayin da za a shiga zai taimaka wajen rage yawan mutanen da ake kwantarwa asibiti a Belgium.
Mutane kusan 690,000 ne suka kamu da cutar COVID-19, wasu fiye da 20,000 kuma suka mutu a kasar Belgium.