Shugaban Sashen Hausa, Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto ya gudanar da taro da kungiyoyin mata da sauran kungiyon matasa domin sauraron kalubalen da suke fuskanta, da kuma cigaban da suke samu a rayuwar yau da kullum a halin da ake ciki da kuma wuraren da su ke.
A wannan taro dai mata da matasan sunkuwa bayyana irin kalubalen da su ke fuskanta iri iri. Hajiya Mairo Ali, wata ‘yar siyasa a bangaren adawa kuma mahaifiyar wata yarinyar da aka ci wa zarafi, na daya daga cikin mahalarta taron, kuma ta ce yayin da ta ke magana da Muryar Amurka idanunta sun cika da hawaye saboda tunawa da yadda aka bata diyarta.
Ta ce shekarun diyarta 12 a yanzu, kuma dan da diyarta din ta haifa ya kai watanni 14. Ta ce kowa fa na so ya ga cigaba tattare da dansa ko diyarsa, sai gashi ana ta bata masu yara a unguwa. Don haka ta ce akwai bukatar gyara a wannan al’amarin.
Ita ko Sarauniyar Matan Birnin Doula, Hajiya Hauwa Sharif Abbas, ta ce a duk lokacin da aka kashe maganar fade da ake yi ma ‘yan mata, ba wai kan yi hakan don kare mutuncin zuri’ar yarinyar ba ne, akan yi hakan ne saboda gudun kar jama’a su yi ma masu kara ganin miyagu saboda kawi an daure mai laifi. Da iyaye da kuma dangin yarinyar sai kawai a rika cewa su miyagu ne; sun sa an kama yaro an daure.
Shi ko Shugaban Kungiyar Matasa na kasar baki daya kuma Turakin Doula, Alhaji Mahmud Yakubu, ya ce wannan taron ya na da matukar muhimmanci saboda wannan ne karon farko da su ka samu damar zama wuri guda da mata su na sauraron matsalolin juna. Ya ce maganganun matan sun sosai masa rai. Y ace a matsayinsu na Shugabanni, za su duba su ga abin da za su yi.
Amma shi kuma Alhaji Abdullahi Salu, Darakta Janar na gidan rediyon nan mai suna Tashar Hausa Bakwai (Tauraruwar Al’umma), ya ce duk gautar fa ja ce. Babbar matsalar Hausawan wurin shi ne kyashi, munafurci, da zargin banza (Ya na ko fadin haka, sai aka barke da tafi). Y ace dole ne a fada wa juna gaskiya tunda abin da aka zo yi kenan. Ya ce don haka Hausa na da yawa amma fa yawan bai da amfani.
Shi ko shugaban wata kungiyar matasa, Liman Abubakar Guri, ya ce kirkiro kungiyoyi da dam aba shi ne mafita ba ga Hausawa. Haka kuma gogayyar zama mai wani matsayi a kungiya ba ta amfani ga jama’a. Ya kuma ja hankalin masu shiga kungiyoyi daban daban da cewa hakan zai hana su amfani ga kansu da kuma jama’a.
Ita kuma wata matashiya, cewa ta yi, duk wadannan matsalolin na faruwa ne saboda rashin wayar da kai yadda ya kamata, musamman ta wajen amfani da kafafen yada labarai. Y ace sai ka ga akwai kungiyon da ke da alaka da batun fifita muradun mata, amma sai ka ga matan ma bas u sani ba saboda rashin yada labari game da kungiyoyin yadda ya kamata. To amma Khalid, wani dan jarida mai zaman kansa, ya ce matasan na yawan fadawa cikin matsaloli ne saboda tsabar son kudi.
Saurari rahoton Garba Awal:
Your browser doesn’t support HTML5