A cewar shugaban sashen hausa Aliyu Mustapha Sokoto dake ziyara yanzu haka a Nijer wannan wani yunkuri ne na kara karfafa dadaddiyar dangantakar dake tsakanin VOA da al’ummar wannan kasa.
A yayin wani kwarya-kwaryan bukin da aka shirya a ofishin Muryar Amurka dake birnin Yamai a karkashin jagorancin shugaban sashen hausa Alhaji Aliyu Mustapha wakilan kungiyoyin da suka hada da kungiyar mata ta FAD da ta mawakan zamani da ta ‘yan jarida da shugabanin makarantar horon ‘yan jarida wato Iftic da na hukumar sadarwa ta CSC.
Darektan kula da sha’anin karatu a makarantar Iftic DE Rabiou Adamou ya yi godiya ga Muryar Amurka sakamakon abinda ya kira karramawa irin ta ban girma.
Haka dai su ma sauran wakilan kungiyoyi da na hukuma suka bayyana farin cikinsu da samun wannan kyauta daga sashen hausa.
Wannan na matsayin wani bangare na ayyukan da shugaban sashen hausa Aliyu Mustapha Sokoto ke gudanarwa a albarkacin ziyarar aikin da ya fara a jamhuriyar Nijer inda a karshen mako zai safka a a Damagaram jihar da ke kan gaba a yawan mutane a wannan kasa.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: